BARIKI IYAWA..πŸ‘„πŸ‘„πŸ’–

/12, 8:25 PM] πŸ’πŸ›πŸ¬SalmaπŸ¬πŸ›πŸ’: [6/2, 5:38 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
1_Tafe take cikin tukun ta na masu isa,da
takama,tamkar mai gudun taka kasa,,hasken
solar,kadai ke haskata da walwalin net din jikin
ta..duk wanda yaci karo da ita,,toh koh ya tsaya
kallon ta,, ko kuma ya wuce yana waiwayen
ta,,wata iriya ce ita.. Allah ya bata abu 3...
Kwarjini...
Kyau,dan akwai zubii.
Sannan uwa uba Aji..
Duk ustazan cinka akaf unguwa da kewayen nan
kasan da zaman ta., sanye take cikin Riga da
skirt na wani rantsatsan farin net,da head blue, ta
zuba wata uwar sarka ta Daham kirar Dubai,,ga
wane shegen takalmi mai tsinin tsiya blue,.rike da
karamar jakar ta blue,, sai katon net data rufa
blue a matsayin gyale,,in ka ganta,zaka rantse da
Allah ko wata yar shugaban kasar ce.. Ba yar Haj
Ladi da Malam Abdu ba..."BARIKI"kenan..wanda
take wa kanta kirari da "IYAWA.
kai da ganin ta zaka gani wani take jira,domin
tana kallon agogon hannun ta tana dan
tsuka,,fuskar nan sai sheki take tasha make up
tamkar wacce zata zaben sarauniyar kyau..harara
ta kwada mishi,lokacin da yai parking din motar a
gaban ta,, anin hali yasa daga nesa ya fara bata
hakuri "Hajiya amini afuwa, wlh go slow na samu,
gashi mai goge motar ne aka kai Matar shi asibiti
kuma ya hana baya nan a bada...tsaki taja kanta
warce mukullin motar ta,," kai kana rasa karyar
kare kanka ne..ji shi a gun,,wlh na kusa sauya
ka...kasan kwa yau ranar nan yadda take a waje
na??ya dukar da kai"Hajjaju ai hakuri..ta bude
pose din ta da bashi dubu1 "kaban waje..tuni ya
kauce ta shiga motar... Tana zama ta duba
mudubin gaban motar, ta Wai waiga cikin
motar,kan ta bude ta dakko air freshener ta
feffesa.." Dan iska,duk ya loda min garadan banxa
a mota tana wari.. Tai tsaki,kan ta daura belt ta
bata key.. Motar ma kamar bata so take Jan
ta..wayan ta ne yai kara..ta dauka,ita kanta
wayan kasan ta manya ce..
"Haba "BARIKI"... wulakancin da zaki min
kenan??8 da kwata fa yanxun... Da sauri ta katse
ta" ee eehm...yi min a hankali.. Gani nan bisa
hanya..tace"Dan ke muka maida abun nan fa
8,kowa yazo amma kujerar ki empty..sannan har
yanxun.. Kit ta kashe wayan"jaraba..mutum sai
mita ya tsohuwa... Ta sanya CD na wakar Ashique
ta taka totur mota ta kara gudu... 15 mint ya
kaita harabar hotel din da zasuyi program din,,tai
parking kan ta fara takun nata na isa..waje ya
hargitse..tamkar wanda ake gidan bikin mata,don
baa gama zama ba,,da Zee ta fara karo da
Royal... Tuni suka hau mata kirarin da ita kadai
suke wa a duk qawaye.. "Yeee...kaga manya a
Baku naku daban... Kaga mai sai maza caroling
mai sa mata su watse...kaga farar
mace..Alkyabba ta mata..wai sukari bakai farin
banza ba..tuni kanta ya fara fashe wa..dan mudin
suka gamu da da qawayen ta yan qarya.. Mai
kirari ta cigaba..ita kwa sai wani juyi take tana
yatsina halamar mai tai lacking.."Dawusu ce
ke..ta kowa dole a kalle ki..in dake a waje dukkan
mata su kauce..Allah ja mana ran suka Sara
mata tare da cewa"BARIKI... Tuni tai wani fari
tare da rausayar da kai ta na kada keys..kan a
hankali ta furta"IYAWA ba..ta barsu nan tai chan
ciki ta zauna kujerar kusa da amarya..suka bita
da kallo...tana kula da Yadda mutum 2 ke Binta
da harara .. amarya da abokin ango..ta kalle shi
ta tabe baki kan ta zauna..

Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[12/22, 4:59 PM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
2_Tamkar ita ake jira kuwa aka fara sanar da
kowa ya zauna a mazaunin shi..
Suka danyi bayanan su..tana ta kula da har
yanxun Harar da Hafeez yake mata.. Ta kada
kai.. Lalle ya kamata tai gaggawar saita mutumin
nan.. Tunda take babu wanda ya taba kokarin
shiga hancin ta sai Hafeez,da kudundune ma ya
shiga shi..tai kwafa dai dai lokacin da aka tashi
amarya da ango zasu yanka cake, chan baya yai
yadda shi kadai ne karshe,, a hankali itama ta
tako,tare da daukar kwalin 5alive tai wajen da
yake..da wannan takun nata, yana ganin ta ya
kara hade rai,, tai murmushin mugun ta, a dai dai
shi ta tsaya kamar zata gogi jikin shi,, yai
tsaki,Yarinyar nan ba karamin tsanar halin ta yai
ba..tunda ya gano ita wacece... Yasan duk macen
kwarai bazata so a kirata da sunan BARIKI
ba..yai tsaki tare da kara matsawa.... Bude kwalin
tai,ta dai daita shi dai dai kafadar shi da gan gan
ta kar kata shi a kafadar, tuni ya fara bulbula
mishi cikin jiki..take yaja baya dan ya tsorata, ga
lemon da sanyi..ya kalle ta ya kalli taron, ba
wanda ke kallon su, an dukufa kallon yankan
cake.. Baisan lokacin da ya sau mata mari ba.,ji
kake"Tasssss,hall ya dauka..abun ka da Babban
waje,tuni ya dauka,,zata dafe kunci da sauri lbrn
wata ya fado mata.. Ana juyo wa ta nuna shi da
hannu.."Wallahi in ka kara sai na maka Marin da
yafi haka... Taja tsaki kan ta juya tai waje tana
dagowa amarya hannu..da mamaki kowa yake
binsu,musamman ango da amarya.. Shi kwa
Hafeez dan tsabar takaici kasa ko motsi yai,..lalle
ya yarda, yarinyar nan "BARIKIN ce da gaske.. Da
sauri yai waje..motar ta yaga ta fita..da sauri ya
shiga tashi,,Ita kwa tana fita data shiga mota ta
sau kuka..tunda take ba mahalukin da ya taba
Marin ta sai Hafeez,, duk da ta maida mishi Marin
kanshi,,......DOMIN SAMUN CI GABA KUYI SUBSCRIBED KO KUMA KU YI MAGANA TA WHATAPP +2347033360730

Comments

Popular posts from this blog

AZABTACCIYAR SOYAYYAπŸ’˜πŸ’˜

AUREN MANUFA 2-4

AUREN MANUFA 2-7 ZUWA 2-9..